- Damuwa da kulawar musulunci game da tsafta da kuma tsarki.
- Wankan Juma'a mustahabbi ne mai ƙarfi don yin sallah.
- Ambaton kai ko da ambaton jiki ya tattaroshi; don ba shi muhimmanci ne.
- Wanka yana wajaba a kan duk wanda aka samu a tare da shi akwai wari abin ƙi wanda mutane suke cutuwa da shi.
- Mafi ƙarfin yini don yin wanka (shi ne) ranar Juma'a don falalarta