- Sunnonin manzanni waɗanda Allah Yake sonsu kuma Ya yarda da su, Yake umarni da su, suna kira zuwa ga cika da tsafta da kyau.
- Halaccin lazimtar waɗannan abubuwan, da kuma rashin rafkana daga garesu.
- Akwai fa'idoji na addini da rayuwa cikin waɗannan ɗabi'un: Daga cikinsu akwai: Kyautata yanayin mutum, da tsaftace jiki, da tabbatar da tsarki, da saɓawa kafirai, da riko (aiwatar da) umarnin Allah.
- Awasu hadisan daban an ambaci ƙarin wasu ɗabi'un banda waɗannan biyar ɗin, kamar: Cika gemu, da asuwaki, da wasunsu.