- Halaccin shafa akan kuffi yana kasancewa ne a lokacin alwala na karamin kari, amma wanka dan babban kari (janaba, al’ada) babu makawa daga wanke kafafuwa.
- shafa yana kasancewa ne sau daya da shudar da hannu mai danshi akan saman kuffin banda kasansa.
- An shardanta shafa akan kuffi ya zama ya sanyasu bayan ya yi cikakkiyar alwala ya wanke kafafuwansa da ruwa, kuma kuffin ya zama mai tsarki, mai suturta bigiren farillar na kafa, kuma shafarsu ya zama a karamin kari ne ba a janaba ba ko abinda yake wajabta wanka ba, kuma shafar ta zama a kayyadajjen lokaci a shari'ance shi ne yini da dare ga mazaunin gari, matafiyi kuma kwana uku da dararensu.
- Ana kiyasta dukkanin abinda yake suturta kafafuwa akan kuffi na jaurabi da wasunsu, to shafa akansu yana halatta.
- Kyakkyawan dabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da koyarwarsa, inda ya hana Mugira ciresu, ya kuma bayyana masa dalili: Cewa shi ya shigar da su suna tsarki; dan ransa ya natsu, ya kuma san hukuncin.