- Tausayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa, da kuma tsoron wahala akansu.
- Asali a umarnin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - (shi ne) wajabci, sai dai inda dalili ya tsayu akan cewa shi nafila ne.
- An so yin asuwaki da kuma (bayanin) falalarsa a yayin kowace sallah.
- Ibnu Daƙiƙul id ya ce: Hikima a mustahabbacin asuwaki a yayin tashi zuwa sallah (shi ne) kasancewarta halin neman kusanci ne zuwa ga Allah, sai ya hukunta ka zama a halin cika da tsafta dan bayyanar da ɗaukakar ibada.
- Gamewar hadisin ya ƙunshi asuwaki ga mai azimi koda bayan zawali ne, kamar salloli biyu: Azahar da la'asar.