- Wannan Hadisin asali ne daga asalin Musulunci, kuma ƙa'ida ne daga ƙa'idojin fiƙihu, ita ce: lallai Yakini ba ya gushewa da kokwanto, asali shi ne wanzuwa a kan abin da ake a kansa, har sai an tabbatar da saɓanin hakan.
- Kokwanto ba ya tasiri a kan alwala, mai sallah yana kan abin yake a kan tsarkinsa muddin dai bai tabbatar da kari (hadasi) ba.