/ Ka musulunta akan abinda ka gabatar na alheri

Ka musulunta akan abinda ka gabatar na alheri

Daga Hakim Dan Hizam - Allah Ya yarda da shi - ya ce:: Na ce: Ya Manzon Allah, kana ganin abubuwan da nake ibada da su a lokacin Jahiliyya na sadaka ko 'yantawa, da sada zumunci, shin a akwai lada? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a agre shi - ya ce: "Ka musulunta akan abinda ka gabatar na alheri".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa idan kafiri ya musulunta to shi ana yi masa sakayya akan abinda ya kasance yana aikatawa a cikin Jahiliyya kafin musuluntarsa na ayyuka na gari kamar sadaka ne ko 'yanta bawa ko sada zumunci.

Hadeeth benefits

  1. Lallai kyawawan ayyukan kafiri a duniya ba za’a yi masa sakayya akansu a lahira ba, idan ya mutu akan kafircinsa.