Daga Ummu Salalmah Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Za'a samu wasu shugaban...
Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa za'a shugabantar da wasu shugabanni akanmu, zamu san wasu daga ayyukansu; dan dac...
Daga Dan Mas’ud - Allah ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Za'a samu babakere da wasu al'am...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu shugabanni zasu shugabanci musulmai, za su yi babakere da dukiyoyin...
Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkaninku masu kiwone to a...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa akwai nauyi akan kowanne musulmi a cikin zamantakewa da zai kula da ita...
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana faɗa a cikin wannan ɗakin nawa :...
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi mummunar addu'a a kan dukkanin wanda ya jiɓinci wani al'amari daga al'amuran musulm...
Daga Tamim al-Dari - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Addini nasiha ne" Muka ce; ga wa? Ya...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa addini a tsaye yake a kan ikhlasi da gaskiya, har a yi kamar yadda Allah...
Daga Ummu Salalmah Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Za'a samu wasu shugabanni zaku sansu kuma zaku yi inkarinsu, wanda ya sani ya kubuta, wanda kuma ya yi inkari ya kubuta, saidai wanda ya yarda ya kuma bi" suka ce: Shin ba ma yakesu ba? ya ce: "A'a, muddin dai suna sallah".
Daga Dan Mas’ud - Allah ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Za'a samu babakere da wasu al'amuran da zaku kisu" suka ce : Ya Manzon Allah mezaka umarcemu? Ya ce: "Ku bada hakkin da ya wajaba akanku, kuma ku roki Allah hakkinku ".
Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkaninku masu kiwone to abin tambayane daga abinda yake kiwonta, shugaban mutane mai kiwo ne shi abin tambayane game da su, mutum mai kiwone ga iyalan gidansa kuma shi abin tambaya ne game da su, mace mai kiwo ce a dakin mijinta da ’yayansa kuma ita abar tambaya ce game da su,, bawa mai kiwo ne akan dukiyar shugabansa shi abin tambaya ne game da ita, ku saurara dukkaninku abin tambaya ne game da abin da aka ba shi kiwonsa".
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana faɗa a cikin wannan ɗakin nawa : "Ya Allah duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tsananta musu, to, ka tsananta masa, duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tausasa musu, to, Ka tausasa masa".
Daga Tamim al-Dari - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Addini nasiha ne" Muka ce; ga wa? Ya ce; "Ga Allah da littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulmai da dukkaninsu".
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta wannan ayar: {Shi ne wanda ya saukar maka da littafi daga gareshi akwai ayoyi bayyanannu su ne mafi yawan littafi da wasu masu kama da juna, amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata sai suke bin abinda yake kama da juna daga gareshi dan neman fitina da neman tawilinsa, kuma babu wanda yasan tawilinsa sai Allah, matabbata a cikin ilimi suna cewa mun yi imani da shi dukkansa daga gurin Ubangijinmu ne, Ba mai tinani sai ma'abota hankula} [Aal Imran: 7]. Ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gareshi to wadannan su ne Allah Ya ambata, to ku gujesu".
Daga Abu Sa'id Al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani".
Daga Nu'uman dan Bashir - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kwatankwacin tsayayye ga iyakokin Allah da mai afkawa cikinsu, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka yi kuri'a a jirgin ruwa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa, wadanda ke kasansa sun kasance idan sun nemi ashayar da su ruwa sai sun wuce wadanda ke samansu, sai suka ce: Dama a ce zamu tsaga wata kafa a rabonmu ba mu cutar da wandanda ke samanmu ba, idan sun barsu da abinda suka yi nufi za su halaka gaba dayansu, idan suka yi riko da hannayensu za su tsira, sai su tsira gaba dayansu".
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya yana da lada kwatankwacin ladaddakin wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga ladansu ba, wanda ya yi kira zuwa ga bata yana da zunubi kwatankwacin zunuban wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga zunubansu ba".
Daga Abu Mas'ud Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: Tafiya ta yanke min, ka ba ni dabbar da za ta ɗaukeni, sai ya ce: "Ba ni da ita", sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan shiryar da shi ga wanda zai ba shi dabbar da za ta ɗaukeshi, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya shiryar a kan wani alheri, to, shi ma yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikatashi".
Daga Sahlu ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce a ranar Khaibara: "Lallai zan bai wa wani mutum wannan tutar Allah Zai yi buɗi ta hannunsa, yana son Allah da manzaonSa kuma Allah da manzonSa suna son shi". Ya ce: Sai mutane suka kwana suna tattaunawa a daran waye a cikinsu za'a ba shi ita, lokacin da mutane suka wayi gari sai suka yi jijjifi ga manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - kowanne su yana ƙaunar a ba shi ita, sai ya ce: "Ina Aliyu ɗan Abi Dalib?" sai aka ce : Shi ya manzon Allah yana ciwon idanu, ya ce: "Ku aike masa", sai aka zo da shi sai manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tofi a cikin (idanuwa) ya yi masa addu'a, sai ya warke kai kace babu wani ciwo a tare da shi, sai ya ba shi tuta, sai (Sayyidina) Aliyu ya ce: Ya manzon Allah, shin zan yake su ne har sai sun zama irinmu? sai ya ce: "Ka zarce a hankali har sai ka sauka a farfajiyarsu, sannan ka kira su zuwa ga musulunci, ka ba su labari da abinda yake wajaba akansu na hakkin Allah a cikinsa, na rantse da Allah, Allah ya shiryar da mutum daya da kai shi ne mafi alheri daga jajayen ni'imomi (rakuma)".
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane, to, yana daga cikinsu".