- Falalar (Sayyidina) Aliyu ɗan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi -, da shaidar manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - gare shi, da son Allah da manzonSa gare shi, da kuma soyayyarsa ga Allah da manzonSa.
- Kwaɗayin sahabbai akan alheri da rige-rigen su gare shi.
- Halaccin ladabi a gurin yaƙi da barin ɗimuwa da daga murya masu tsoratarwa waɗanda babu buƙatuwa zuwa gare su.
- Daga dalilan annabtar - tsira daa mincin Allah su tabbata agare shi - bada labarinsa da samun nasara akan Yahudawa, da warkar da idanuwan Aliyu ɗan Abi Dalib a hannunsa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da izinin Allah.
- Cewa manufa mafi girma a yaƙI ita ce shigar mutane cikin musulunci.
- Da'awa tana kasancewa da bi asannu-sannu sai a nema daga kafiri a farko ya shiga cikin muslunci ta hanyar furta kalmar shahada biyu, sannan a umarce shi da farillan musulunci bayan hakan.
- Falalar Da’awah zuwa musulunci da abinda ke cikinta na alheri ga wanda aka kira da mai kiran, wanda aka kira zai iya shiriya, mai kiran kuma za’a ba shi lada mai girma.