/ Wanda ya shiryar a kan wani alheri, to, shi ma yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikatashi

Wanda ya shiryar a kan wani alheri, to, shi ma yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikatashi

Daga Abu Mas'ud Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: Tafiya ta yanke min, ka ba ni dabbar da za ta ɗaukeni, sai ya ce: "Ba ni da ita", sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan shiryar da shi ga wanda zai ba shi dabbar da za ta ɗaukeshi, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya shiryar a kan wani alheri, to, shi ma yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikatashi".
Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Wani mutum ya zo ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Lallai cewa dabbata ta halaka, ka ɗorani a kan wata dabbar, kuma ka ba ni wani abin hawan da zai kai ni, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ba shi uzuri cewa ba shi da wani abin da zai dorashi a kansa, sai wani mutum da ya ke wurin ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan shiryar da shi ga wanda zai ba shi dabbar da za ta ɗaukeshi, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa ya zama abokin tarayyar mai sadakar a lada; domin ya shiryar da mabuƙacin zuwa gareshi.

Hadeeth benefits

  1. Kwaɗaitarwa a kan shiryarwa ga aikin alheri.
  2. Kwaɗaitarwa ga aikata alheri yana daga sabubban taimakekeniya ga zamantakewa da kuma cikarsa.
  3. Yalwar falalar Allah - Maɗaukakin sarki -.
  4. Hadisin ƙa'ida ne mai gamewa, yana shiga kowa ne ayyukan alheri.
  5. Idan mutum bai sami damar tabbatar da buƙatar mai tambaya ba, to, ya shiryar da shi ga waninsa.