- Hadisin yana daga alamomin Annabcinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda ya bada labarin abinda zai kasance a cikin al'ummarsa sai ya afku kamar yadda ya bada labari.
- Halaccin sanar da wanda aka jarraba da abinda zai afku gareshi na bala'i; dan ya yi wa kansa tanadi idan ta zo masa, zai zama mai hakuri mai neman lada.
- Riko da Alkur’ani da sunna mafitane daga fitintinu da sabani.
- Kwadaitarwa akan ji da bi ga shugabanni da kyautatawa, da rashin tawaye garesu, koda zalinci ya afku daga garesu.
- Anfani da hikima da bin sunna a lokaci fitintinu.
- Ya wajaba ga mutum tsayuwa da hakkin dake kansa koda wani abu na zalinci ya faru akansa.
- A cikinsa akwai dalili akan ka'idar: Ana zabin mafi saukin sharruka biyu ko mafi saukin cutuka biyu.