- Muhimmancin horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki a kiyaye zamantakewar jama'a da kuma tsiransu.
- Daga hanyoyin koyarwa akwai buga misalai, dan kusanto da ma'anoni ga hankula kamar ga abin.
- Aikata abin ki a zahiri tare da kin yin inkari akansa barna ce da zata cutar da kowa da kowa.
- Halakar jama'a tana kasance wa ne akan barin ma'abota barna suna barna a bayan kasa.
- Aiki na kuskure da kyakkyawan niyya ba sa isuwa a gyaruwar aiki.
- Nauyin aiki a cikin jama'ar musulmi na gaba daya ne, ba'a rataya shi ga wani ayyananan mutum.
- Azabtar da kowa da kowa saboda zunuban wasu mutane idan ba a yi hanani ba.
- Masu aikata mummunan aiki suna bayyanar da mummunan aikinsu mai makon su yi alheri ga jama'a kamar munafukai.