Daga Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin mutuwarsa da (darare) biyar alhali shi...
Annabi - tsira da amincinAllah su tabbata a gare shi - ya sanar game da darajarsa a wurin Allah - Madaukain sarki -, kuma cewa ita takai mafi kololuwa...
Daga Abu Hayyaj Al’asadi, ya ce: Aliyu Ɗan Abi Talib, ya ce da ni: Shin ba na aika ka ba a kan abin da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbat...
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana aika sahabbansa a kan kada su bar ((mutum-mutumi)) na wani abu da yake da rai aka...
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya ce: "Canfi shirka ne, canfi sh...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargadi daga canfi shi ne canfi daga kowanne abu, abin ji ne ko abin gani, daga tsuntsaye...
Daga Imaran Ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Ba ya cikimmu wanda ya yi...
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi alƙawarin narkon azaba ga wanda ya aikata wasu ayyuka cikin al’ummarsa, da ya ce: Ba ya daga...
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Babu ciratar cuta kuma babu camfi, fatan a...
Annabi - tsira da amincin Allah agare shi - yana bada labarin cewa ciratar cutar da mutanen Jahiliyya suke ƙudircewa da cewa cuta tana cirata da kanta...

Daga Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin mutuwarsa da (darare) biyar alhali shi yana cewa: "Lallai ni ina barranta zuwa ga Allah da ya zama ina da badadi daga cikinku, to lallai cewa Allah - Madaukakin sarki - hakika Ya rike ni badadi, kamar yadda Ya riki (Annabi) Ibrahim badadi, da na kasance mai rikon badadi daga al'ummata da na riki Abubakar badadi, ku saurara lallai wadanda suka gabace ku sun kasance suna maida kaburburan Annabawansu da salihansu masallatai, ku saurara kada ku maida kaburbura masallatai, lallai ni ina hanaku hakan".

Daga Abu Hayyaj Al’asadi, ya ce: Aliyu Ɗan Abi Talib, ya ce da ni: Shin ba na aika ka ba a kan abin da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aike ni ba?? Kada ka bar mutum-mutumi sai ka share shi, haka kabari da aka ɗaga shi sai ka daidaita shi (da sauran kaburbura).

Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya ce: "Canfi shirka ne, canfi shirka ne, canfi shirka ne, - sau uku -", babu wani a cikinmu saidai, saidai cewa Allah - Mai girma da daukaka - Yana tafiyar da shi da dogara (ga Allah).

Daga Imaran Ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Ba ya cikimmu wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi, ko ya yi bokanci ko aka yi masa bokanci, ko ya yi tsafi ko aka yi masa tsafi. Duk wanda ya ƙulla wani ƙulli, duk wanda ya je wurin boka ya gasgata shi a kan abin da ya faɗa, to, ya kafircewa abin da aka saukar ga (Annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Babu ciratar cuta kuma babu camfi, fatan alkairi yana birgeni" ya ce: A ka ce : Menene fatan alkairi? sai ya ce: "Magana mai dadi".

Daga Zaidu Dan Khalid AlJuhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba a Hudaibiyya a bayan (ruwan daya sauka) a wannan daren da ya wuce, lokacin da ya sallame sai ya juya ya fuskanto mutane, ya ce: "Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumini da kafiri sun wayi gari daga bayina" Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Ubangiji da rahamarSa, to wannan ya yi imani da Ni, kuma ya kafircewa taurari. Amma wanda ya ce: Da tauraro kaza da kaza, to wannan ya kafirce mi Ni kuma ya yi imani da taurari".

Daga Uƙuba ɗan Amir Aljuhani - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane sun fuskanto gare shi , sai ya yi wa tara daga cikinsu caffa (Mubaya’a) yaki yi wa ɗaya, sai suka ce: Ya Manzon Allah, ka yi wa tara caffa ka bar wannan? ya ce: "Atare da shi akwai laya". Sai ya shigar da hannunsa sai ya yanketa, sai ya yi masa caffa, ya ce: "Wanda ya rataya laya to haƙiƙa ya yi shirka".

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Lallai cewa tawaida da layu da tiwala (tsafin juyar da tunani musamman tsakanin ma'aurata) shirka ne".

Daga wasu cikin matan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba.

Daga Abdullahi Dan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji wani mutum yana cewa: A'a na rantse da Ka'abah, sai Dan Umar ya ce: Ba'a rantsuwa da wanin Allah, domin cewa ni na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka".

Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu".

Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin wasu mutane daga Ash'arawa ina neman ya dauki nauyinmu, sai ya ce: "Wallahi ba zan dauki nauyinku ba, bani da abinda zan dauki nauyinku" Sannan muka zauna lokacin da Allah Ya so, sai aka zo da wasu rakuma, sai ya yi mana umarni da rakuma uku, lokacin da muka tafi sai sashinmu suka ce da sashi: Allah ba Zai yi mana albarka ba, mun zowa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - muna neman ya dauki nauyinmu sai ya yi rantsuwa cewa ba zai dauki nauyinmu ba sai kuma ya dauki nauyinmu, sai Abu Musa ya ce: sai muka zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai muka ambata masa hakan, sai ya ce: "Ba nine na ɗauki nauyinku ba, a’a Allah ne Ya ɗauki nauyinku, Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai inga waninta mafi alheri daga gareta. sai na yi kaffarar rantsuwata, kuma nazowa wanda shi ne mafi alherin".