- Haramcin rantsuwa da wanin Allah - Maɗaukakin sarki -, kuma daga cikin hakan: amana, kuma hakan yana daga ƙaramar shirka.
- Amana ta ƙunshi ɗa'a da bauta da ajiya da bayarwa hannu da hannu da amintarwa.
- Rantsuwa bata ƙulluwa sai da Allah - Maɗaukakin sarki - ko da wani suna daga sunayenSa ko wata siffa daga siffofinSa.
- AlKhaɗɗabi ya ce: Wannan yana kama da karhancin ya zama saboda cewa shi ya yi umarni a yi rantsuwa da Allah ne da kuma siffofinSa, amana kuwa ba ta daga siffofinSa, kawai ita wani al'amari ce daga aumarninSa, kuma farilla ce daga farillanSa, sai aka hanasu su rantse da ita dan abinda ke cikin hakan na daidaitawa tsakaninta da tsakanin sunayen Allah - Mai girma da ɗaukaka - da kuma siffofinSa.