- Kiyaye tauhidi da aƙida daga abin da yake ɓata su.
- Haramta yin amfani tawaida ta shirka da layu da tiwala.
- Ƙudirewar mutum a waɗannan abubuwa ukun cewa su sabubba ne: Shi ne shirka ƙarama; domin ya sanya abin da ba sababi ba ne a matsayin sababi, amma idan ya ƙudire cewa suna amfanarwa kuma suna cutarwa a kan kansu, to, shi shirka ne babba.
- Gargaɗi a kan aikata sabubba na shirka da kuma ababen haramtawa.
- Haramta (nau'o'in) tawaida kuma suna daga shirka, sai dai abin da aka shara'anta daga cikinsu.
- Ya kamata a rataya zuciya ga Allah Shi kaɗai, cuta da amfani daga gareshi ne Shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, ba mai zuwa da alheri sai Allah, kuma ba mai tunkuɗe sharri sai Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Tawaida da ta halatta ita ce wacce ta tattaro sharuɗɗa uku; 1- Ya ƙudire cewa su sababi ne ba sa amfanarwa sai da izinin Allah. 2- Ta kasance da Al-ƙur'ani da kuma sunayen Allah da siffofinSa da addu'o'in Annabi da wasu ababen shara'antawa. 3- Ta zama da yare abin fahimta, kuma kada ta ƙunshi ɗalasimai (saƙandamai) da sha'awazah (surkulle).