- Dogaro ga Allah - Madaukakin sarki -, kuma ba mai zuwa da alheri sai Allah, kuma ba mai tunkude sharri sai Allah.
- Hani daga camfi, shi ne abinda mutum yake camfa shi, kuma yake hana aiki.
- Fata na gari ba shi daga cikin camfin da aka hana, kawai shi yana daga yi wa Allah - Madaukakin sarki - kyakkyawan zato ne,
- Kowanne abu yana faruwa ne da ikon Allah - Mai girma da daukaka - Shi kadai baShi da abokin tarayya.