- Haramcin bokanci, da zuwa wurin boka da kuma tambayarsu gaibu.
- Tabbas ana hanawa mutum ladan biyayya don ya zama uƙuba a gare shi a kan aikata laifi.
- Yana shiga cikin wannan Hadisin abin ake cewa burji da duba shi, da karanta tafin hannu, da ƙwarya, ko da kuwa leƙawa ne kaɗai, domin duka yana cikin bokanci, kuma yana cikin iƙirarin sanin gaibu.
- Idan wannan ya zama sakamakon wanda ya je wurin mai duba, to, ya ya halin shi mai duban.??
- Sallar kwanaki arba’in idan ya yi ba ta yi ba, kuma ba zai rama ta ba, saidai babu ladanta.