Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku ce : Allah Ya so wane ma ya s...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya ce a zancensa: Allah Ya so wane ma ya so", ko Allah Ya so da wane; hakan do...
Daga Mahmud Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi tsoron abin...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mafi yawan abinda yake jin tsoronsa ga al'ummarsa: Karamar shirka ita ce...
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wani mutum ba zai jefi wani...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi cewa wanda ya cewa wani: Kai fasiƙine, ko: Kai kafiri ne, idan ya kasance bai zam...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Abu biyu a cikin mutane su kafi...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da ɗabi'u biyu a cikin mutane suna daga ayyukan kafirai, da kuma ɗabi'un...
Daga Abu Marsad Alghanawi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Kada ku zauna a kan ka...
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana zama a kan kaburbura.
Kamar yadda ya hana yin Sallah ana kallon kaburbura, ta yadda kab...
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku ce : Allah Ya so wane ma ya so, saidai ku ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so".
Daga Mahmud Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya, Allah - Mai girma da daukaka - Zai ce da su a ranar Alkiyama idan za’a yi wa mutane sakayyar ayyukansu: Ku tafi zuwa ga wadanda kuka kasance kuna nuna musu ayyukanku a duniya, sai ku duba shin zaku samu wani sakamako a wurin su?".
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wani mutum ba zai jefi wani mutum da fasiƙanci ba, kuma ba zai jefe shi da kafirci ba, sai ta dawo kansa idan m'abocinta bai zama kamar hakan ba".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Abu biyu a cikin mutane su kafirci ne a cikinsu: Sukar nasaba, da kukan kera ga mamaci".
Daga Abu Marsad Alghanawi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu.
Daga Abu Ɗalha - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai kare ko hoto a cikinsa".
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Mala'iku ba sa tafiya da ayarin da a cikinsa akwai kare ko ƙararrawa".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shaidan yana zo wa dayanku sai ya ce: Waye ya halicci kaza? waye ya halicci abu kaza? har ya ce: Waye ya halicci Ubanugijinka? idan ya ga haka to (sai) ya nemi tsarin Allah ya kuma hanu".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: ""Lallai Allah Ya ce: Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da shi, kuma bawaNa bai taba kusanta zuwa gare Ni ba da wani abu kamar abinda na farlanta masa ba, bawa Na ba zai gushe ba yana kusanta gareNi da nafilfili har sai Na soshi, idan Naso shi zan zama jinsa da yake ji da shi, da ganinsa da yake gani da shi, da hannunsa da yake dauka da shi, da kafarsa da yake tafiya da ita, kuma da zai rokeni sai na ba shi, kuma da zai nemi tsari da Ni sai Na tsare shi, kuma ban taba kai komo a kan yin wani abu kamar karbar ran mumini ba, yana kin mutuwa Ni kuma iNa ki masa wahalarsa"
Daga Irbad dan Sariya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu, sai ya yi mana wa'azi, wa'azi isasshe zukata suka ji tsoro daga gare shi, idanuwa suka zubar da hawaye daga gareshi, aka ce: Ya Manzon Allah ka yi mana wa'azin bankwana to ka yi mana alkawari.
Sai ya ce: 'Na horeku da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne mutumin Habasha, za ku ga sabani mai tsanani a bayana, to na horeku da sunnata da sunnar Halifofina shiryayyu, ku rike su da turamen hakoranku, na haneku da fararrun al'amura, domin cewa kowacce bidi'a bata ce".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a sai ya mutu, to, ya mutu irin mutuwar Jahiliyya, wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin makauniyar tuta, yana fushi saboda ƙabilanci, ko yake kira zuwa ƙabilanci, ko yake taimakon ƙabilanci, sai aka kashe shi, to, kisa ne na Jahiliyya, wanda ya yi fito na fito da al'ummata yake dukan mutumin kirkinta da fajirinta, ba ya kiyaye wa tsakanin mumininta, kuma ba ya cika alkawari ga ma'abocin alkawari (kafirin amana), to, wannan ba ya tare da ni, ni ma ba na tare da shi".
Daga Ma'aƙil ɗan Yasar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Babu wani bawa da Allah Zai ba shi kulawar wani abin kiwo, ya mutu a ranar da zai mutu alhali shi yana algus ga abin kiwonsa sai Allah Ya haramta masa aljanna".