- Haramcin riƙon kare sai dai karen farauta ko gadin dabbobi ko gona.
- Riƙon hotuna suna daga al'amura munana waɗanda mala'iku suna guduwa daga garesu, kuma samunsu a guri sababi ne na haramcin rahama, kwatankwacin haka a kare.
- Mala'ikun da ba sa shiga gidan da a cikinsa akwai kare ko hoto sune mala'ikun rahama, amma masu gadin (mutane) da wasunsu daga waɗanda suke da wani aiki kamar mala'ikan mutuwa to su suna shiga kowane gida.
- Haramcin rataya hotonan masu rayuka a bangwaye da wasunsu.
- AlKhaɗɗabi ya ce: Kaɗai mala'iku basa shiga gidan da a cikinsa akwai kare ko hoto daga abinda riƙonsa yana haramta na karnuka da hotuna, amma abinda ba haramun bane na karen farauta da gona da kiwo, da hoton da ake wulaƙantasu a shinfiɗu da matasai da wasunsu to shigar mala'iku ba ya haramtuwa saboda shi.