- Wannan Hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudusi ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu kususiyyar Alƙur'ani a cikinsa, waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, na bauta da karanta shi, da alwala saboda shi da tahaddi (fito na fito) da gajiyarwa (I’ijazi) da wanin hakan.
- Hani daga cutar da waliyan Allah da kwaɗaitarwa a son su, da iƙirari da falalarsu.
- Umarnin gaba da maƙiya Allah da haramta jiɓintarsu.
- Wanda ya yi da'awar walittaka ba tare da bin shari'ar Allah ba to shi maƙaryaci ne a da'awarsa.
- Ana samun walittaka a wurin Allah ne ta hanyar aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta.
- Daga sabubban son Allah ga bawa da amsa Addu’ar sa aikata nafilfili bayan tsayuwa da wajibai da barin abubuwan da aka haramta.
- Nuni akan ɗaukakar waliyyai da ɗaukakar matsayinsu.