- Wannan narkon bai keɓanci babban shugaba ba da mataimakansa, kai, shi mai gamewa ne a dukkanin wanda Allah Ya ba shi kiwon wani abin kiwo.
- Wajibi a kan dukkanin wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin musulmai ya yi musu nasiha, kuma ya yi ƙoƙari wajen ba da amana, kuma ya kiyayi ha'inci.
- Girman nauyin da ke wuyan dukkanin wanda ya jiɓinci wani abin kiwo mai gamewa, ko keɓantacce, babba ne ko ƙarami ne.