- Hani daga daukar karnuka da tafiya da su, in banda karen farauta ko na gadi.
- Mala'iku wadanda ba sa tafiya da (karnuka da kararrawa) su ne Mala'ikun rahama, amma masu rubuta ayyukan bayi to su ba sa rabuwa da bayi a zamansu da tafiye-tafiyensu.
- Hani daga ƙararrawa; Domin cewa ita garayace daga garayoyin shaidan, kuma a cikinta akwai kamanceceniya da gangar kiristoci.
- Ya wajaba akan musulmi ya yi kwadayi akan nisanta da dukkanin abinda sha'aninsa shi ne nisantar da mala'iku daga gare shi.