- Bijirewa daga wasiwasin Shaidan da darshe-darshen sa da rashin tunani a kan su, da fakewa zuwa ga Allah - Madaukakin sarki a cikin tafiyar da su.
- Dukkanin abinda yake afkuwa a cikin zuciyar mutum na wasuwasin da ya sabawa shari'a to daga Shaidan ne.
- Hani daga tinani a cikin zatin Allah, da kwadaitarwa akan tunani a abubuwan halittarSa da kuma ayoyinSa.