- Hana yin sallah a maƙabartu, ko tsakanin kaburbura, ko ana kallon kaburbura, sai dai Sallar janaza kamar yadda hakan ya tabbata a Sunnah.
- Hana yin Sallah ana kallon kaburbura don toshe ƙofar kaiwa ga shirka.
- Musulunci ya hana wuce iyaka a kan kaburbura ya kuma hana wulaƙantasu, ba wuce iyaka, kuma ba wulaƙantawa.
- Alfarmar Musulmi tana nan bayan rasuwarsa, saboda faɗin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Karya ƙashin mamaci kamar karya shi yana raye ne.