- Wajabcin tsarkake aiki saboda Allah - Mai girma da daukaka - da gargadarwa daga riya.
- Tsananin tausayinsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa, da kwadayinsa akan shiriyarsu da kuma nasiharsa garesu.
- Idan wannan ya zama shi ne tsoronsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi alhali shi yana yiwa sahabbansa magana kuma su ne shugabannin salihai to tsoro akan wanda ke bayansu ya fi tsanani.