Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutum yana kan Addinin abokinsa, sabod...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum yana kamanceceniya da abokinsa amintacce a rayuwarsa da kuma al'adarsa, k...
Daga Mugira Ɗan Shu'uba - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wasu jama'a daga al'ummata ba z...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu mutane ba za su taɓa gushewa ba daga al'ummata suna masu rinjaye akan...
Daga Tamimud Dari -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Lallai wannan al'amarin...
Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wannan addinin zai game dukkan sasannin ƙasa, duk gurin da dare da rana...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Musulunci ya fara yana baƙo, k...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Musulunci ya fara yana baƙo a cikin ɗaiɗaikun mutane da kuma ƙarancin ma'a...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na rantse da wanda ran Muhammad y...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rantsuwa da Allah cewa wani daya daga wannan al'ummar ba zai ji shi ba, Bayahude ne ko Ki...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutum yana kan Addinin abokinsa, saboda haka dayanku ya duba wanda zai yi abokantaka (da shi)".

Daga Mugira Ɗan Shu'uba - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wasu jama'a daga al'ummata ba za su gushe ba suna masu rinjaye, har sai al'marin Allah ya zo musu alhali su suna masu rinjaye».

Daga Tamimud Dari -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Lallai wannan al'amarin zai kai inda dare da rana suka kai, kuma Allah ba Zai bar wani gidan bulo ko na gashi ba sai Allah Ya shigar da wannan addinin cikinsa, da girman mai girma ko da ƙasƙancin kaskantacce, buwaya ce da Allah Yake ɗaukaka musulunci da ita, da ƙasƙancin da Allah Yake ƙasƙantar da kafirci da shi" Tamimi al-Dari ya kasance yana cewa: Haƙiƙa na san hakan a iyalan gidana, haƙiƙa wanda ya musulunta a cikinsu alheri da ɗaukaka da buwaya ya same shi, wanda yake kafiri a cikinsu kuma ƙasƙanci da wulaƙanci da jiziya sun same shi .

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Musulunci ya fara yana baƙo, kuma zai dawo baƙo, aljanna ta tabbata ga baƙi».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da zai ji ni Bayahude ne ko Kirista, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba sai ya zama cikin 'yan wuta".

Daga Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce a washegarin jifan babban shaidan alhali shi yana kan taguwarsa: "Ka tsintomin tsakwankwani". sai na tsinto masa tsakwankwani bakwai, su tsakwankwani ne na harbi, sai ya fara yana motsasu a tafinsa yana cewa: "Misalan wadananan sai ku yi jifa (da su)”. sannan ya ce: "Yaku mutane na haneku da wuce gona da iri a addini, kadai wuce gona da iri a addini shi ya halaka wadanda ke gabanku".

Daga Abdullahi Dan Mas'ud ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Masu tsanantawa sun halaka" ya fadi hakan ne har sau uku.

Daga Adi Dan Hatim daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Yahudawa an yi fushi da su, Kiristoci kuwa batattu ne".

Daga Abdullahi dan Amr dan Amr dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah Ya rubuta abinda ya kaddarawa halittu kafin Ya halicci sammai da kasa da shekara dubu hamsin, ya ce: Al’ArshinSa yana kan ruwa".

Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi -: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zantar damu alhali shi mai gaskiya ne abin gasgatawa: "Lallai cewa halittar dayanku ana tarota a cikin mahaifiyarsa yini arba'in da dare arba'in. Sannan ya zama gudan jini tamkarsa, sannan ya zama gudan tsoka tamkarsa, sannan a aiko masa da Mala'ika, a yi masa izini da kalmomi hudu, sai ya rubuta arzikinsa da ajalinsa da aikinsa, dan wuta ne ko dan Aljanna ne, sannan ya busa rai a cikinsa. Lallai dayanku zai yi aiki da aikin 'yan Aljanna har ya zama tsakaninsa da ita bai zamo ba sai zira'i, sai littafi ya rigaya agare shi sai ya yi aiki da aikin 'yan wuta sai yashiga wutar. Kuma cewa dayanku zai yi aiki da aikin 'yan wuta har ya kasance tsakaninsa da ita bai zamo ba sai zira'i, sai littafi ya rigaya akansa, sai ya aikata aikin 'yan aljanna sai ya shigeta".

Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Aljanna ita ce mafi kusa daga dayanku daga igiyar takalminsa, wuta ma tamkar hakan".

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "An kewaye wuta da sha'awowi, kuma an kewaye Aljanna da abubuwa ki".