- Bada bayanin kasantuwar baƙuntar Musulunci bayan yaɗuwarsa da kuma shahararsa.
- A cikinsa akwai alama daga alamomin Annabci, inda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari da abinda zai faru a bayansa, sai ya faru kamar yadda ya bada labari da shi.
- Falalar wanda ya ƙauracewa ƙasarsa da danginsa; saboda Musulunci, kuma lallai aljanna ta tabbata agare shi.
- Baƙi su ne waɗanda suke gyaruwa idan mutane suka ɓaci, kuma sune waɗanda suke gyara abinda mutane suka ɓata.