- Umarni da abokantaka da zababbu da kuma tsabosu, da hani daga abokantaka da mutanen banza.
- An kebanci aboki banda ɗan'uwa; domin aboki kai ne wanda ka zabe shi, amma ɗan'uwa da makusanci to kai baka da zabi a cikinsa.
- Zabin aboki babu makawa dole sai an yi tunani.
- Mutum yana karfafar addininsa ta hanyar abokantakar muminai, kuma yana raunana shi ta hanyar abokantaka da fasikai.