/ Masu tsanantawa sun halaka

Masu tsanantawa sun halaka

Daga Abdullahi Dan Mas'ud ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Masu tsanantawa sun halaka" ya fadi hakan ne har sau uku.
Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labari game da tabewar masu tsanantawa - ba tare da shiriya da ilimi ba - a addinin su da duniyar su, da kuma maganganun su da ayyuakan su, masu ketare iyakar shari'a da su wanda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi.

Hadeeth benefits

  1. Haramcin tsanantawa da dorawa kai abinda ba zai iyaba a cikin al'amura gaba dayan su, da kwadaitarwa akan nisantarhakan a kowane abu; musammanma a cikin ibadu da girmama salihai.
  2. Neman mafi cika a cikin ibadu da wasunsu al'amari ne abin yabo; kuma yana kasancewane ta hanyar bin shari'a.
  3. Son karfafa al'amari mai muhimmanci; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya maimaita wannan jumlar har sau uku.
  4. Martabar musulunci da kuma saukinsa.