- Daga sabubban afkawa a sha'awowi kawatawar Shaidan abin ki da mummuna, har rai ya gan shi mai kyau ne, sai ya karkata zuwa gare shi.
- Umarni da nisantar sha'awowin da aka haramta; domin cewa su hanya ce zuwa wuta, da kuma hakuri akan abubuwan ki; domin cewa su hanya ce ta zuwa Aljanna.
- Falalar yakar rai ko kokari a ibada, da kuma hakuri akan abubuwan ki da wahalar da ke kewaye ayyukan biyayya.