- Gamewar sakon Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zuwa dukkanin halittu, da wajabcin binsa, da shari'arsa ta shafe dukkanin shari'o'i.
- Wanda ya kafirce da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata aagre shi - ikirarins na imani da waninsa daga Annabawa - tsira da aminci ya tabbata agare su baki daya - ba zai amfanar da shi da komai ba.
- Wanda bai ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba, kuma sakon musulunci bai isa zuwa gare shi ba to shi yana da uzuri, al'amarinsa a lahira yana ga Allah - Madaukakin sarki -.
- Amfanuwa da musulunci yana tabbata koda kafin mutuwa ne, koda a halin tsananin rashin lafiya ne, muddin dai rai bai kai makogwaro ba.
- Inganta Addinin kafirai - daga cikinsu akwai yahudawa da kiristoci - kafirci ne.
- Ambaton yahudawa da kiristoci - a cikin hadisin - dan fadakarwa ne akan wasunsu; hakan domin cewa yahudawa da kiristoci suna da littafi, idan hakan ya zama sha'aninsu, to wasunsu daga wadanda ba su da littafi ya fi cancanta, dukkaninsu shiga Addininsa da biyayya gareshi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zama dole akansu.