- Wajabcin yin imani da hukunci da kaddara.
- Kaddara ita ce : Sanin da Allah ya yi wa abubuwa da rubuta su da ganin damarSa da kuma halittar su da ya yi .
- Imani da cewa kaddarori ababen rubutawane tun kafin halittar sammai da kasa yana haifar da yarda da mika wuya.
- Lallai cewa Al’Arshin Ubangiji ya kasance akan ruwa tun kafin halittar sammai da kasa.