Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a abin da yake ruwatowa daga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - cewa Yace: "Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, kada ku yi zalunci, ya ku bayina dukkaninku ɓatattu ne sai wanda Na shiryar da shi, ku nemi shiriyata in shiryar da ku, ya ku bayina, dukkaninku mayunwata ne sai wanda Na ciyar, ku nemi ciyarwata in ciyar da ku, ya ku bayina dukkaninku matsiraita ne sai wanda na tufatar da shi, ku nemi tufatarwata zan tufatar da ku, ya ku bayina lallai kuma yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai duka, ku nemi gafarata; Zan gafarta muku, Ya ku bayania haƙiƙa ba za ku iya cutar da ni ba, ballantana ku cuceni, ba za ku iya amfanata ba, ballantana ku anfanar da Ni, ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da muatnenku da aljanunku za su kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai ƙara komai daga mulkina ba, Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su kasance a kan zuciyar mafi fajircin mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai rage wani abu daga mulkina ba, Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su tsaya a bigire ɗaya su tambayeni, sai in ba kowa tambayarsa hakan ba zai rage komai daga abin da ke wurina ba, sai dai abin da allura take tauyewa idan an shigar da ita kogi, Ya ku bayina kaɗai ayyukankun ne ina kiyayesu gareku, sannan in cika muku su, to, wanda ya sami alheri, to, ya godewa Allah wanda ya samu wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa".