Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya daukaka - Ya faɗi cewa: Ya haramta zalunci a kan kansa, kuma Ya sanya zalunci abin haramtawa a tsakanin bayinsa, kada wani ya zalunci wani. Kuma cewa halitta gaba ɗayansu ɓatattu ne daga hanyar gaskiya sai da shiriyar Allah da dacewarsa, wanda ya roketa zai datar dashi kuma ya shiryeshi, kuma cewa halitta mabuƙata ne zuwa ga Allah masu buƙata ne gareshi a dukkanin buƙatunsu, wanda ya roƙi Allah zai biya buƙatarsa Ya kuma isar masa, kuma cewa suna yin zunubai dare da rana, kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Yana suturtawa yana yafewa a yayin roƙon bawa gafara, kuma cewa su ba za su iya cutar da Allah ba, ko su amfanar da Shi da komai ba, kuma da ace sun kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya, to, takawarsu ba za ta ƙara komai a mulkin Allah ba, da sun kasance a kan mafi fajircin zuciyar mutum ɗaya, to, fajircinsu ba zai tauye komai daga mulkinsa ba; domin cewa su raunana ne mabuƙata a gurin Allah, masu buƙatuwa zuwa gareshi a kowane hali da zamani da wuri, Shi ne Mawadaci - tsarki ya tabbatar masa -. kuma cewa da ace sun tsaya a bigire ɗaya mutanensu da aljanunsu, na farkonsu da na ƙarshensu suna roƙon Allah sai Ya ba wa kowane ɗaya daga cikinsu abin da ya roƙa, hakan ba zai tauye komai daga abinda ke wurin Allah ba, kamar allura ce da ake shigar da ita kogi sannan a fitar da ita, to, kogin ba zai ragu da komai ba, wannan don cikar wadatarsa tsarki ya tabbatar masa.
Kuma Allah - tsarki ya tabbatar masa Yana kiyaye ayyuakan bayi, Yana tsaresu musu su, sannan Ya cika musu su a ranar al-ƙiyama, wanda ya samu sakamakon aikinsa alheri, to, ya godewa Allah a bisa dacewa da ya yi ga biyayya gareshi, wanda ya samu sakamakon aikinsa wani abu saɓanin hakan, to, kada ya zargi kowa sai zuciyarsa mai yawan umarni da mummuna wacce ta ja shi zuwa taɓewa.