Allah Zai damke kasa, Zai ninke sammai da hannunSa na dama, sannan Ya ce: Ni ne sarki, ina sarakunan kasa
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah Zai damke kasa, Zai ninke sammai da hannunSa na dama, sannan Ya ce: Ni ne sarki, ina sarakunan kasa".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Madaukakin sarki - a ranar Alkiyama Zai damke kasa Ya tattarota, Ya ninke sama da hannunSa na dama Ya ninke sashinta a saman sashi Ya tafiyar da ita Ya karar da ita, sannan Ya ce: Ni ne sarki, ina sarakunan kasa?!
Hadeeth benefits
Tinatarwa da cewa mulkin Allah Shi ne wanzajje kuma mulkin waninSa mai gushewa ne.
Girman Allah da girman ikonSa da sarautarSa da cikar mulkinSa.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others