- Kamanta mukallafi da ɗan kasuwa, lafiya kuma da rarar lokaci da jari; wanda ya kyautata amfani da jarinsa to zai samu kuma za ci riba, wanda ya tozartar da shi zai yi hasara da nadama.
- Ibnu Khazin ya ce: Ni'ima ita ce abinda mutum yake ni'imtuwa da ita kuma yake jin daɗinta, kamunga kuwa ita ce mutum ya sayi (abu) da ninkin kuɗinsa, ko ya siyar da ƙasa da farashi irin nasa; wanda jikinsa ya samu lafiya kuma ya shagaltu da ƙoƙari bai sami sarari dan gyara lahirarsa ba to shi kamar wanda aka yi wa kamunga ne a cikin ciniki.
- Kwaɗayi akan amfanuwa lafiya da kuma rarar lokaci dan neman kusanci ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da kuma aikata alherai kafin kufcewarsu.
- Godewa ni'imomin Allah yana kasancewa ne da yin amfani da su a cikin biyayya ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Alƙali Abubakar ɗan Arabi ya ce: An yi saɓani a cikin farkon ni'imar Allah akan bawa, aka ce: Imani, kuma an ce: Rayuwa, an ce kuma: Lafiya, na farkon ya fi domin cewa shi ni'ima ce kai tsaye, amma rayuwa da lafiya to cewa su ni'ima ce ta duniya, kuma basa kasancewa ni'ima ta haƙiƙa sai idan ta kasance da imani, to a wannan lokacin za’a yi wa mutane da yawa kamunga a cikinsu, wato ribarsu zata tafi ko ta ragu, wanda ya sakarwa ransa mai umarni da mummuna mai dawwamarwa zuwa hutu sai ya bar kiyayewa akan iyakokin (Allah), da lazimta akan ɗa'a to haƙiƙa an yi masa kamunga, haka nan idan ya zama mai rarar lokaci, domin cewa wanda aka shagaltar zai iya kasancewa yana da uzuri sabanin mai rarar lokaci; cewa shi uzuri zai dauke daga gare shi kuma hujja ta tsayu a kansa.