- An so sallama akan abinda Hadisi ya zo da shi, idan mai tafiya a kasa ya yi sallama ga wanda ke kan abin hawa da makamancin hakan daga abinda aka ambata, to ya halatta, sai dai cewa shi sabanin abinda yafi ne.
- Yada sallama akan siffar da ta zo a cikin Hadisi yana daga sabubban soyayya da kauna.
- Idan sun kasance daidai a cikin abinda aka ambata, to mafificinsu shi ne wanda ya fara sallama.
- Cikar wannan shari'ar a cikin bayanin dukkan abinda mutane suke bukatarsa.
- koyar da ladubban sallama da bawa kowanne mai hakki hakkinsa.