- Halaccin rantsuwa ba tare da ansa a yi rantsuwa ba; dan karfafa labari koda ya kasance a nan gaba ne.
- Halaccin togaciya da fadinsa: In Allah Ya so", bayan rantsuwa, kuma togaciya idan an yi niyya tare da rantsuwa, kuma hakan ya kasance a hade da rantsuwar to kaffara bata wajaba akan wanda ya yi karya rantsuwarsa.
- Kwadaitarwa a kan sabawa rantsuwa idan ya ga waninta shi ne mafi alheri daga rantsuwar, kuma ya yi kaffarar rantsuwarsa.