- Haramcin suranta abubuwa masu rai, domin suna cikin hanyoyin shirka.
- Shar’antuwar gusar da mummunan abu da hannu ga wanda yake da doka ko iko a kan haka.
- Kwaɗayin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a kan gusar da duk wasu alamomi na maguzanci na hotuna da mutum mutumi da gine gine a kan kaburbura.