- Wajibcin dogaro ga Allah, da imani da abin da Allah Ya hukunta Ya kuma ƙaddara. Da kuma haramcin camfi da asiri da bokanci, ko tambayar masu yin haka.
- Iƙirarin sanin gaibu ɓangare ne na shirka, wanda yake kore Tauhidi.
- Haramcin gasgata bokaye da zuwa wurinsu, kuma yana shiga nan duba a tafin hannu, da kwarya da buruji da nazari a kansu, ko da kuwa don leƙawa ne.