- Hadisn asali ne a bayanin matakan canja abin ki.
- Umarni da bi sannu-sannu a hani ga abin ki, kowa gwargwadon iyawarsa da ikonsa.
- Hani daga abin ki wani babi ne mai girma a Addini kuma ba ya saraya akan wani mutum, kuma ana dorawa kowanne musulmi shi gwargwadon ikonsa.
- Umarni da aikin alheri da hani daga abin ki yana daga dabi'un imani, kuma imani yana karuwa yana kuma raguwa.
- Ana sharadantawa a hani daga abin ki: Sanin cewa wannan aikin abin ki ne.
- Ana sharadantawa a canja abin ki: Cewa kada wani abin kin mafi girma daga gare shi ya biyo baya.
- Akwai wasu ladubba da sharuddan da yake kamata ga musulmi ya sansu ga hani daga abin ki.
- Hani daga abin ki yana bukatuwa zuwa ga siyasa ta shari'a, kuma da ilimi da basira.
- Rashin inkari da zuciya yana nuni ga raunin imani.