- Falalar kira zuwa shiriya, kadan ce ko da yawa, kuma cewa mai kira yana da ladan mai aikin, hakan yana daga girman falalar Allah da cikar karamcinSa.
- Hadarin kira zuwa ga bata kadan ce ko da yawa, kuma mai kiran yana da zununubi kwatankwacin zunubin wanda ya aikata.
- Sakamako yana daga jinsin aiki, wanda ya yi kira zuwa alheri yana da ladan wanda ya aikata shi, wanda ya yi kira zuwa ga sharri yana da zunubi kwatankwacin zunubin wanda ya aikata shi.
- Ya wajaba akan musulmi ya kiyayi a yi koyi da shi dan bayyanar da sabonsa ga mutane suna kallonsa, cewa shi zai yi laifi da wanda ya kwaikwayeshi koda bai zaburar da shi akan hakan ba.