- Yana wajaba a kan wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amuran musulmai da ya tausasa musu gwargwadon iyawa.
- Sakamako yana kasance daga jinsin aikin da aka yi.
- Ma'aunin abinda ake lura da shi wajen tausayi da tsanani shi ne muddin dai bai saɓawa Al-Qur'ani da Sunna ba.