- Ya wajaba ga mai hankali ya yi gaggawar tuba, kuma kada ya lamuncewa kamun Allah, idan ya kasance wanda yake kan aikata zalunci.
- Jinkirtawar da Allah Yake yi wa azzalumai da kuma rashin gaggauta yi musu uƙuba ɗaurin talala ne garesu, da kuma ninka musu azaba idan ba su tuba ba.
- Zalunci yana cikin sabubban uƙubar Allah ga al’umma.
- Idan Allah Ya halakar da gari, to, zai iya yiwuwa akwai mutanen ƙwarai a ciki, to, su waɗannan za’a tashe su a ranar Alkiyama a kan abin da suka mutu akan shi na kyakkyawan aiki, ba zai cutar da su ba dan wannan ukubar ta hada da su.