- An so wanke hannaye kafin shigar da su a cikin ƙwarya (butar Alwala) a farkon alwala, ko da bai kasance ya taso daga barci ba, idan ya farka daga barcin dare ne, to, ya wajaba a wankesu.
- Ya kamata ga mai koyarwa ya bi hanya mafi kusa ga fahimta da tabbatar da ilimi ga mai koyo, daga hakan akwai koyarwa a aikace.
- Ya kamata ga mai sallah ya tunkuɗe duk wasu tunani dake rataye da shagulgulan duniya, cikar sallah da kamalarta (yana tabbata ne) a halartowar zuciya a cikinta, in ba haka ba fa, to, kuɓuta daga tunani iri daban daban yana da wahala [a sallah], ya wajaba a kansa ya yaƙi ransa kada ya yi sako-sako a hakan.
- An so damantawa a alwala.
- Shar’antuwar jerantawa a tsakanin kuskurar baki da shaƙa ruwa da facewa.
- An so wanke fuska da hannaye da ƙafafuwa sau uku, amma wajibi (shi ne) sau ɗaya.
- Gafarar Allah ga abin da ya gabata daga zunubai ya jerantu ga al'amura biyu: Alwala, da sallah raka'a biyu, a kan siffar da aka ambata a hadisin.
- A kwai iyaka ga kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwala: Iyakar fuska:
- Tun daga matsirar gashin kai na al'ada, zuwa abin da ya sauka zuwa gemu da haɓa a tsawo, a faɗi kuma daga kunne zuwa kunne. Iyakar hannu: Tun daga gefen 'yan yatsu zuwa gwiwar hannu, shi ne mararraba tsakanin sangalalin hannu da damtse.
- Iyakar kai kuma: tun daga matsirar gashi na al'ada daga sasannin fuska zuwa saman wuya, shafar kunnuwa suna cikin kai. Iyakar ƙafa: Dudduge gabaɗayansa tare da mararraba tsakaninsa da ƙwauri.