Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau biyu-biyu
Daga Abdullahi ɗan Zaid - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau biyu-biyu.
Buhari ne ya rawaito shi
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance a wasu lokutansa idan zai yi alwala yana wanke Kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwalarsa sau biyu, sai ya wanke fuska - daga cikin wankewar akwai kuskurar baki da shaƙa ruwa - da hannaye da ƙafafuwa sau biyu.
Hadeeth benefits
Wajibi a wanke gaɓɓan alwala (shi ne) sau ɗaya abin da ya ƙaru, to, shi mustahabbi ne.
Halaccin alwala sau bibiyu a wasu lokutan.
Abin shar'antawa a shafar kai (shi ne) sau ɗaya.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others