- Wajabcin wanke kafafuwa a alwala; domin da shafa ya halatta da wanda ya bar wanke karshen kafa ba'a yi masa narko da wuta ba.
- Wajabcin game dukkan gabban da ake wankewa da wankewa da ruwa, kuma wanda ya bar wani sashi karami daga abinda ya wajaba a wanke shi da gangan da kuma sakaci to sallarsa ba ta inganta ba.
- Muhimmancin ilimantar da jahili da kuma shiryar da shi.
- Malami ya yi inkarin abinda yake gani na tozartar da farillai da sunnoni ta hanyar da ta dace.
- Muhammad Ishak al-Dahlawi ya ce: Cika (alwala) nau'i uku ne: Farilla shi ne game gaba da (ruwa) sau ɗaya, da sunna shi ne wankewa sau uku, da kuma mustahabbi shi ne tsawaitawa tare da wankewa sau uku.