Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga bandaki zai ce: "Ya Allah ni ina neman tarinKa daga Shaidanu maza da Shaidanu mata
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga bandaki zai ce: "Ya Allah ni ina neman tarinKa daga Shaidanu maza da Shaidanu mata".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin shiga gurin da zai biya bukatarsa a cikinsa, fitsarine ko bayan gida, zai nemi tsarin Allah, kuma zai fake gareShi da ya kareShi daga sharrin Shaidanu maza da mata, An fassara khubs da kahaba'is kuma da sharri da kuma najasa.
Hadeeth benefits
An so yin wannan addu'ar a yayin nufin shiga bandaki.
Dukkanin halitta masu bukatuwa ne zuwa Ubangijinsu na a tunkude abinda yake cutar da su a kowanne yanayi.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others