- Wajabcin gaggawa zuwa horo da aikin alheri, da fadakar da wanda bai sani ba da rafkananne, musamman ma idan barnar ta kasance lalacewar ibadarsa za ta kasance akan akan barnar.
- Wajabcin game gabban alwala da ruwa, kuma cewa wanda ya bar wani yanki daga gaba - koda ƙarami ne - alwala ba ta ingantuwa daga gare shi, kuma sakewa ce ta wajaba idan ya jima kafin ya gani.
- Halaccin kyautata alwala, hakan ta hanyar cikata da kyautata akan yadda aka yi umarni da ita a shari'ance.
- Kafafuwa biyu suna daga gabban alwala, kuma shafa ba ta isuwa a cikinsu, kawai babu makawa sai an wanke su.
- Jerantawa, yana kamata tsakanin gabban alwala, ta yadda zai wanke kowacce gaba kafin ta gabaninta ta bushe.
- Rashin sani da mantuwa ba sa sarayar da wajibi, kawai suna sarayar da zunubi ne, wannan mutumin wanda bai kyautata alwalarsa ba saboda rashin sani, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi bai sarayar masa da wajibi ba, wato alwala, kawai ya umarce shi ya saketa.