- Asalin Addini shi ne imani da Allah da UbangidantakarSa da AllantakarSa da sunayenSa da siffofinSa.
- Muhimmancin tabbatuwa bayan imani, da kuma ci gaba a cikin ibada, da tabbata akan hakan.
- Imani sharadi ne na karbar ayyuka.
- Imani da Allah, ya kunshi abinda kudire shi yake wajaba daga akidun imani da tushensu, da abinda yake bin hakan, daga ayyukan zuciyoyi, da jawuwa da mika wuya ga Allah a badini da zahiri.
- Tabbatuwa lazimtar hanya ce, ta hanyar aikata wajibai da barin abubuwan da aka hana.