- An shar'antawa dukkan wanda ya farka daga bacci ya face hanci dan gusar da gurbin Shaiɗan daga hancinsa, idan ya kasance zai yi alwala, to umarnin ya fi ƙarfafuwa a lokacin.
- Face hanci yana daga cikar fa'idar shaƙa ruwa; domin shaƙa ruwa tsarkake cikin hanci ne, facewa kuma hakan yana fitar da datti tare da ruwan.
- Ƙayyade shi da baccin dare, dan yin riƙo daga lafazin "yana kwana"; domin kwana ba ya kasancewa sai daga baccin dare, kuma cewa shi ne lokacin zatan tsawaitawa da zirfafawa.
- A cikin hadisin akwai dalili akan cakuɗuwar Shaiɗan ga mutum alhali shi ba ya jin hakan.